Thursday, May 8
Shadow

Ji dalilin da ya sa farashin fetur bai faɗi ba a Najeriya ba duk da faɗuwar sa a kasuwar duniya

Dillalan man fetur da masana sun bayyana dalilan da suka sa ba a ganin sauƙin kirki na man fetur a gidajen mai duk da faɗuwar fashin gangar mai a kasuwar duniya.

Ƴan Najeriya a yanzu na sayen man fetur tsakanin N940 zuwa N970 a Abuja babban birni ƙasar.

Farashin gangar ɗanyen mai ya sauka a kasuwar duniya sakamakon yakin kasuwanci da shugaba Trump na Amurka ya ƙaddamar kan China da sauran ƙasashen duniya, inda ake sayar da ganga kan dala 61 zuwa 65.

Kodayake a ranar Laraba farashin ɗanyen man ya ƙaru bayan sabbin takunkuman Amurka kan man Iran da ake shigar wa China.

Rikicin haraji ya rage buƙatuwar man fetur a duniya saboda raguwar samar da abubuwa, dalilin da ya sa man fetur ya yi arha a Najeriya da sauran ƙasashe.

Sai dai kuma wasu na ganin ya kamata sauƙin ya fi wanda ake gani idan aka yi la’akari da faɗuwar darajar gangar mai a duniya.

Duk da Najeriya ce kasar da fetur ya fi sauki a kasashen yammacin Afrika amma wasu yan kasar na ganin ya kamata idan man ya sauka a kasuwar duniya a ga tasirinsa a gidajen sayar da man.

Karanta Wannan  Kamata yayi ka yi hakuri ka barwa dan kudu ya tsaya takara a 2027>>Wasu 'yan PDP daga kudu suka gayawa Atiku

Amma masanin tattalin arzkin albarkatun man fetur a Najeriya, Dr Ahmad Adamu ya ce yadda dala ke tsada ba za a iya ganin ragin kirki ba duk da faɗuwar farashin gangar mai a duniya.

“Ana iya samun ragi a farashin gangar mai a duniya, amma kuma a samu ƙari a wani wurin saboda tasirin farashin dala, idan da dalar Amurka ake cinikayyar man”

“Amma idan da tsarin naira ne ake sayen man, za a iya ganin gagarumin sauyin farashi, a duk lokacin da farashin gangar ɗanyen mai ya sauka a kasuwar duniya,” masanin.

Ita ma a nata ɓangaren kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya Ipman ta ce duk da cewa matatar Dangote ta rage farashin man fetur amma kuma idan farashin dala na ci gaba da tsada ba za a iya ganin ragin kirki ba a gidajen mai.

“Ba za a ga wani ragin farashin kirki a gidajen mai tun lokacin da aka ce sai Dangote ya saye mai da dala.”

Karanta Wannan  Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa - Badaru

“Amma yanzu tun da gwamnati ta ce Dangote zai saye da naira, za a ci gaba da ganin saukin farashin man,” in ji Shugaban kungiyar Ipman Abubakar Maigandi Shettima.

A ranar Laraba Dangote ya sanar da rage N40 na farashin man fetur a matatarsa daga N865 zuwa N835.

“Saboda haka za mu rage farashi idan mun dauki man mai sauki.,” a cewar shgaban Ipman

Yankasuwar man sun ce ribarsu ta dogara ne da yadda suka yi saurin sayar da man inda suka yi watsi da zargin cewa suna boyewa ne har sai ya yi tsada.

Sai dai ana zargin yan kasuwar da tsula farashi duk da cewa da sauki suka samu man fetur din.

Abu uku da ke tasiri a farashin mai a Najeriya

Masana dai na ganin dala ce ke tantance makomar farashin fetur a Najeriya saɓanin faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Saukar farashin mai a Najeriya ya dogara ne saukin farashin dalar Amurka da kuma saukar farashin gangar ɗanyen mai sannan za a iya ganin tasirin fara

Karanta Wannan  Obasanjo ya bayyana cewa a zamanin mulkin Marigayi shugaban kasa, Umar Musa 'Yar'adua Dangote yaso Gwamnati ta sayar masa da matatar man Fatakwal data Kaduna amma 'Yar'adua yaki yadda

Dr Ahmad ya ce saukar farashin gangar ɗanyen mai a duniya kawai bai isa a ga wani babban tasirinsa ba a gidajen mai a Najeriya

“Amma idan darajar dala ce ta faɗi, kuma ɗanyen mai ya tsaya yadda yake, za a iya ganin babban tasiri a kasuwar mai a Najeriya domin da dala ake sayen man.”

Za a fi ganin tasirin farashi a gidajen mai a Najeriya idan darajar dala ce ta faɗi,” a cewar Dr Ahmad.

Masanin ya ce ba ya tunanin gidajen mai da gangan suke ƙin rage farashi a Najeriya, domin a cewarsa “hamayyar kasuwanci ta sa kowa na son ya riga sayarwa”

“Zan fi ɗora laifin kan dala da take ƙara tsada”

Ya ce duk yadda ake son saukin farashin mai a Najeriya dole sai idan farashin dala ya sauka.

Masanin a ƙara da cewa danyen mai zai iya sauka amma tasirin ba wani abin a zo a gani ba ne sai idan dala ta sauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *