Friday, December 5
Shadow

Ji ‘Dalilin da ya sa rabin farashin wake ya faɗi a Najeriya’

Ƙungiyar manoman wake a Najeriya ta bayyana amfani mai yawa da suka samu a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da suka jawo raguwar farashinsa a kasuwanni a baya-bayan.

Shugaan ƙungiyar ta Cowpea and Beans Farmers, Processors and Marketers Association of Nigeria (C&BFPMAN), Kabir Shuaibu ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa suna farin ciki da saukar farashin.

Rahoton na NAN ya ce daga wata ukun ƙarshe na 2024, farashin babban buhun wake mai nauyin 100kg ya kai har N210,000 zuwa N240,000, a madadin N90,000 da aka dinga sayar da shi a 2023.

Sai dai kuma, daga wata ukun farko na 2025 zuwa yanzu farashin ya sauka sosai zuwa N80,000 ko N120,000 – ya danganta da nau’insa.

Karanta Wannan  Ji yanda aka kama Wata Babbar mace me danwake data yiwa Almajiri me shekaru 14 fyàdè a jihar Bauchi

“Muna farin ciki da saukar farashin waken. Mun samu ninki 10 na abin da muka saba samu a shekarun baya,” kamar yadda Kabiru ya shaida wa NAN.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *