Friday, December 5
Shadow

Ji Dalilin da yasa shugaba ‘yan siyasa ke ta tururuwa zuwa gidan Tinubu dake Legas

Rahotanni sun bayyana cewa gidan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dake Legas ya zama kamar wata makkar ‘yan siyasa.

Inda suke ta tururuwa dan zuwa ganinsa tun bayan da ya fara hutun Sallah a can.

Tinubu ya je Legas ranar 27 ga watan Mayu inda ya halarci taron kungiyar ECOWAS sannan daga nan ya kaddamar da wasu ayyuka sannan ya fara hutun Sallah.

Daga cikin manyan ‘yan siyasar da suka kaiwa shugaba Tinubu ziyara akwai;

Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang.

Fasto Tunde Bakare.

Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.

Gwamnan jihar Osun, Senator Ademola Adeleke.

Sai kuma Ministan kasafin Kudi, Atiku Bagudu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon:An kama wani magidanci Da ya Dirqawa diyarsa cikin shege a jihar Yobe

masana dai sun ce ganin Tinubu a Legas yafi sauki fiye da ganinsa a Abuja, sannan da maganar zaben 2027 na daga cikin dalilan da ‘yan siyasr ke ta tururuwa zuwa gidan shugaban kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *