Friday, December 5
Shadow

Ji sabon mukamin da Shugaba shugaba Tinubu ya baiwa Ganduje bayan sauka daga shugaban APC

Rahotanni sun ce shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin baiwa tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje sabon mukami.

Hakan na zuwane kwana daya da saukat Ganduje daga mukamin shugaban jam’iyyar APC.

Wata majiya ta bayyanawa jaridar Vanguard cewa, Shugaban kasa Bola Tinubu kwanannan zai bayyana Ganduje a matsayin jakadan Najeriya zuwa kasar waje.

A kwanakin baya dama an yada rade-radin cewa, Shugaba Tinubu na shirin baiwa Ganduje mukamin jakadanci amma maganar ta lafa.

Wasu majiyoyi sun ce Ganduje a wancan lokacin ya ki karbar mukamin jakadane saboda yana jan zarensa a matsayin shugaban jam’iyyar APC wanda yana ganin kujerar shugaban jam’iyya tafi karfin ta Jakada.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda wata mata ta lakadawa dansandan Najeriya dukan kawo wukaa tsakiyar titi

Da yawa a wancan lokaci sun yi mamakin irin karfin da Ganduje ke dashi a gwamnatin Tinubu da har za’a bashi mukami amma yaki karba kuma shugaban kasa ya kyakeshi.

Saidai yanzu ta faru ta kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *