Friday, December 26
Shadow

Ji ta’asar da zaratan Tshàgyèràn Dhàjì 3 sukawa wata karamar yarinya a jihar Naija

Wasu ‘yan Bindiga 3 sun yiwa karamar yarinya me shekaru 13 fyàdè a kauyen Kudodo dake yankin Galko na karamar hukumar Shiroro jihat Naija.

Wani dan jam’iyyar APC a jihar Naija, Babangida Wassa Kudodo ne ya bayyana hakan.

Yace lamarin ya nuna irin yanda rashin tsaro ke kara munana a jihar.

Tuni aka kai yarinyar Asibiti dan kula da lafiyarta.

Jihar Naija na daga cikin jihohin Arewa masu fama da matsananciyar matsalar tsaro.

Karanta Wannan  Gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya na taro kan tsaro a yankin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *