Tuesday, May 6
Shadow

Ji yanda ‘Ƴàn bìndìgà ke ci gaba da ɗora wa al’umma haraji a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun saka harajin miliyoyin naira ga wasu al’umomi da ke yankin Ɗan Kurmi a ƙaramar hukumar mulki ta Maru.

Ƴanbindigar sun ayyana Laraba a matsayin ranar wa’adin biyan kuɗin amma tuni suka fara aiwatar da dokar tsare mutane a garin Zargado har sai an biya kudin a matsayin diyya.

Al’ummar yankin da abin ya shafa sun sheda wa BBC cewa sun samu kansu a wannan tasku ne bayan da wasu mazauna yankin suka kona daji da kuma hare-haren da sojoji suka kai wa ‘yanbindigan shi ne barayin dajin suka dora musu wannan haraji na naira miliyan 60.

Honarabul Iliyasu Salisu Dankurmi ya tabbatar wa da BBC wannan lamari :

”Sojoji sun shigo aiki wannan yanki sun koma to kuma yanzu ‘yanbindiga sun zo sun aza mana haraji, suka ce sai mun biya wannan dukiyoyin da aka hallaka musu,” in ji shi.

Karanta Wannan  Hukumomin sojin Amurka sun sace kudin da aka ware dan ciyar da sojojin kasar Abinci

Suka ce, ”abin da suka zama mana naira miliyan 60 kuma idan ba mu biya ba za mu fuskanci matsaloli fiye da yanda muka fito baya.”

Ya ce ‘yanbindigan sun sanya musu wa’adin zuwa ranar Laraba.

Al’ummomin sun ce ba wani mataki da za su iya dauka domin ‘yanbindigan sun fi su karfi.

Bayanai sun ce ‘yanbindigan har ma sun fara kama mutanen wani gari, Zargado, inda zuwa lokacin hada wannan labari sun kama musu mutum takwas da cewa sai an biya wannan kudi naira miliyan 60 za su sake su.

Al’ummomin sun ce sun sanar da hukuma, sun fadi halin da suke ciki amma kuma babu wani mataki da hukuma ta dauka har yanzu.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta yi gargadin a daina cin Ganda

Shi ma Ubankasa na garin Dankurmi, Alhaji Sani Usman, ya tabbatar wa da BBC lamarin.

”Lokacin da aka aza wannan kudin yankunan su ne, Manya da Kaboso da Yalwa da Bafadanmakini da Huda da Dargazo da Danhayan-dargazo da Koloma,” in ji shi.

Ya yi karin bayani da cewa, ”Kuma kamar yadda muka samu labarin wani kauyen daga ciki sun sanya wa daji wuta su kuma ‘yanbindigan suka ce lalle sai sun aza wa wadannan kauyukan hudu daga cikinsu kowa ne sai sun biya wannan kudi.”

Sai dai kuma Ubankasar ya ce bai san wa’adin da ‘yanbindigan suka sanya wa jama’ar ba.

Karanta Wannan  Hukumar EFCC na tsaka mai wuya inda aka samu jami'anta da sace kudade da kadarorin da aka kwato daga ma'aikatan Gwamnati

Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yanbindigan wadanda suka addabi yankuna a wasu jihohin yankin arewa maso yamma, da suka hada da jihar ta Zamfara da Sokoto da Kebbi da, wasu jihohin na arewacin Najeriya, irin wannan haraji ba.

Barayin dajin kan hana mazauna yankunan karkara noma da kiwo da ma zama a garuruwansu ba, inda suke kashe mutane da dama da sacewa da kuma barna dukikoyinsu ba.

Suna kuma hallakawa da kama mutane da dama da sunan karbar kudin fansa, duk da matakan da hukumomin kasar ta Najeriya ke cewa suna dauka, inda lamarin kusan ya gagara shawo kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *