
Wani dan majalisar tarayyar Najeriya yawa abokan aikinsa Tonon Silili inda yace babu dan majalisar dake samun kasa da Naira Biliyan 2 na yiwa mazabarsa aiki a majalisar dattijai.
Yace hakanan a bangaren ‘yan majalisar wakilai, babu wanda ke samun kasa da Naira Biliyan 1 shima dan yiwa ‘yan mazabarsa aiki.
Ya bayyana hakane a jihar Osun, kamar yanda jaridar Sahara reporters ta ruwaito.
Saidai ba’a bayyana sunansa ba, yace ‘yan majalisar sun samu karin kudinne bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur.
Hakanan yace suma Gwamnoni an kara musu kudaden da ake basu na yiwa jihohinsu aiki.
Wannan dai ya zowa mutane da mamaki ganin yanda ‘yan majalisar ke kukan suma suna cikin wani hali a yayin da ‘yan Najeriya ke kokawa da tsadar rayuwa.