
Wani dan Najeriya ya cirewa dan sandan kasar Malaysia kunne ta hanyar cizo bayan da aka kamashi a wani Asibiti.
An kama dan Najeriyar ne a Metro Prima, Kepong, Kuala Lumpur, Malaysia.
Shugaban ‘yansandan birnin Kuala Lumpur Datuk Rusdi Mohd Isa ya tabbatar da kamen inda yace sun kama dan Najeriyar ne bayan da aka kirasu aka shaida musu cewa wani dan kasar waje ya tayar da hankali a wani Asibiti.
Ya kara da cewa, lamarin ya farune ranar Juma’a da misalin karfe 10:03 na safe April 25, 2025.
Yace bayan an kama mutumin me shekaru 38, an hadashi da dansanda ya kaishi Ofis inda aka ajiyeshi a bayan mota da ankwa a hannunsa.
Saidai a hakanne ya kama kunnen dansandan ta baya ya cizge.
Yace an kai dansandan Asibiti yayin da shi kuma wanda ake zargi ana ci gaba da bincike akansa.