
Kasar Ukraine ta kama wannan dan Najeriyar da yaje yanawa kasar Rasha yaki.
Fadan Ukraine da Rasha dai ya ki ci yaki cinyewa inda ake daukar mutane daga kasashen Duniya daban-daban dan su taya kasashen yaki.
Rahoton yace sunan dan Najeriyar da aka kama din Kehinde Oluwagbemileke dan kimanin shekaru 29.
Kuma Tuni aka kaishi gidan yari.
Rahoton yace Kehinde Oluwagbemileke an kamashi ne da safarar kwaya a kasar Rasha, to maimakon yayi zama gidan yarin, shine ya zabi ya je yayiwa kasar ta Rasha yaki dan a rage masa shekarun zaman gidan yarin da za yi.
Rahoton yace Kehinde Oluwagbemileke daya ne daga cikin ‘yan kasashen waje dake taya kasar Rasha yaki, kuma kamin a kamashi ya shafe watanni 5 yanawa kasar ta rasha yaki.
An yi kira ga gwamnati data dauki matakin hana ‘yan Najeriya zuwa kasar ta Rasha dan tayata yaki.