
Matar sojan Najeriya Lt. Samson Haruna ta kasheshi ta hanayar cimma nasa wuta bayan da fada ya kaure tsakaninsu.
Lamarin ya farune a Bassey Barracks, dake Ibagwa, karamar hukumar Abak dake jihar Akwa-Ibom.
Lamarin ya farune ranar Sept. 22, 2025.
Sojan wanda likita ne, sun samu zazzafar muhawara da matarsa me suna Mrs. Samson Haruna wanda hakan yasa ta yi amfani da fetur ta babbakeshi.
Sojan ya samu raukuna sosai inda nan da nan aka garzaya dashi zuwa Asibiti.
Bayan da aka je Asibitin ya rasu acan.
An kama matar inda yanzu haka ake kan bicikenta.