
Rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo tsaiko a shari’ar da ake wa tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako bisa zargin satar Naira Biliyan 29.
Ana shirin yon sulhu tsakanin gwamnatin tarayya a wajan kotu da Murtala Nyako amma sai mutuwar Buhari ta kawo tsaiko.
A ranar Juma’a ne ya kamata ace an ci aba da shari’ar ta Nyako amma ragin zuwan babban lauyan gwamnati, Prince Lateef Fagbemi (SAN) ya kawo tsaiko a shari’ar.
Dan haka ne mai shari’a Justice Peter Lifu ya dage shari’ar sai zuwa 25 ga watan Yuli kamin a ci gaba.
Kotun tace itama tana sane da kwanaki 7 na jimamin rasuwar Buhari da Gwamnatin tarayya ta ware.