
A ci gaba da shari’ar da akewa tsohon Ministan sufuri jiragen sama a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Hadi Sirika, Wani shaida da EFCC ta gabatar yawa tsohon Ministan Tonon Silili.
A ranar 9 ga watan Mayu ne EFCC ta gurfanar da Hadi Sirik, da diyarsa, Fatima, da mijin diyarsa, Jalal Sule Hamma da kamfaninsu me suna Al Buraq Global Investment Ltd bisa zargin almundahanar kudaden kwangila wadda ba’a yi aikin ba.
An gurfanar da su ne a babbar kotun tarayya dake Abuja inda ake kuma zargin Tsohon Ministan da baiwa kamfanin da diyarsa da mijinta suka mallaka kwangila.
Shaidan me suna Christopher Odofin ya gayawa kotun cewa aikin na yin gini ne a filin jirgin dake jihar Katsina wanda kuma kamfani daya ake son yayishi.
Saidai Hadi Sirika ya raba kwangilar zuwa gida biyu inda ya baiwa wani kamfani me suna Enginos Nigeria Limited rabin aikin na Naira Biliyan 1.3 sannan ya haiwa kamfanin diyarsa da mijinta Al Buraq Global Investment Ltd dayan bangaren kwangilar na naira Biliyan 1.4.
Shaidan yace diyar Hadi Sirika ma’ikaciyace a kamfanin mai na kasa, NNPCL sannan mijinta ma ma’ikacin gwamnatin tarayya ne amma haka suka hada hannu suka bude kamfanin.
Yace kuma ministan ya baiwa kamfanin diyar tasa duka kudin aikin warau Naira Biliyan 1.4 duk da cewa ba’a yi aikin ba.
An dage ci gaba da shari’ar sai nan da 27 ga watan October inda EFCC zata sakw gabatar da wasu shaidun.