Sanata Osita Ngwu dake wakiltar mazabar Enugu West a majalisar dattijai ya yabi kyawun Bianca Odumegwu-Ojukwu wadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aike da sunanta majalisar dan a tantance ta a matsayin karamar Ministar harkokin kasashen waje.
A yayin da ya tashi zai mata tambaya, ya fata cewa kyakkyawa, Bianca.
Nan take kuwa kakakin majalisar, Godswill Akpabio ya taka masa burki inda yace ya daina yabon kyawunta dan babu inda ta rubuta cewa ita kyakkawan ce a cikin takardunta.
Hakan yasa an fashe da dariya a majalisar.