Sunday, March 16
Shadow

Ji yanda ‘yan Bìndìgà suka yi shiga irin ta EFCC suka je wani Otal suka kwashe mutanen ciki a jihar Naija

Yan Bindiga masu garkuwa da mutane sun yi basaja inda suka yi shiga irin ta jami’an hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC suka shiga otal din White Hill Hotel dake Chanchaga a jihar Naija suka yi garkuwa da mutane.

Lamarinnya farune ranar Talata February 27, 2025 da misalin karfe 4:58 na dare.

‘Yan Bindigar sun lalata kyamarorin CCTV dake ital din kamin suka shiga daki-daki suka dauki mutane akalla 10 suka yi awon gaba dasu

Hukumar ‘yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan kokarin gano wadanda suka yi wannan aika-aika da kuma kubutar da wadanda aka sace.

Karanta Wannan  Ba gudu ba ja da baya akan maganar cire tallafin man fetur dana dala

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *