
Jihar Kebbi na son saka dokar kisa ga masu baiwa masu garkuwa da mutane bayanan sirri.
Gwamnan jihar, Comrade Nasiru Idris yace zasu saka dokar kisa ko kuma daurin rai da rai ga masu baiwa masu garkuwa da mutanen bayanan sirri.
Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara kauyukan Tadurga da Zuru da Kyebu inda ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda ‘yan Bindiga suka kashe.
Kauyukan na kananan hukumomin Danko/Wasagu dake jihar kuma kwanannan aka kai hare-hare wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 30 da kuma sace shanu da yawa.
Gwamnan ya bayyana cewa, zasu dauki matsalar tsaro da matukar muhimmanci a jihar.