
Jihohin Bauchi da Katsina sun bayar da hutun Watan Azumin Ramadana ga ‘yan makaranta.
A jihar katsina, bayan kulle makarantun Gwamnati, Hukumar HISBAH ta jihar ta kuma fitar da sanarwa ga masu marantu masu zaman kansu dasu kulle makarantun nasu har sai bayan Azumin watan Ramadana.
Kwamandan HISBAH na jihar, Aminu Usman ne ya fitar da sanarwar inda yace rashin yiwa wannan doka biyayya zai sa a hukunta duk makarantar da aka kama suna karatu.
Hakanan a jihar Bauchi na, mahukuntan jihar sun bayar da hutu daga ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa ranar 5 ga watan Afrilu ga makarantu.