
Rahotanni daga gabas ta tsakiya na cewa kasashen Larabawa na cikin wadanda suka tare jirage marasa matuka 100 da kasar Iran ta jefawa Israyla a matsayin martani.
Kasashen Larabawan da suka tare wadannan makamai sun hada da Saudi Arabia, Jordan, Qatar, Turkiyya, UAE.
Sannan kuma akwai kasar Azerbaijan, da Israyla, da Amurka, da Ingila.
Rahotanni sun ce sai da Israyla ta kwace iko da dukkanin sararin samaniyar kasar Iran tana cin karanta babu babbaka da jiragen yakinta.