Friday, December 5
Shadow

Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga kan layin dogo

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinja da ya taso daga Abuja babban birnin Najeriya zuwa Kaduna ya faɗi a ranar Talata da safe.

Lamarin dai ya jefa fargaba a tsakanin fasinjoji da ke cikin jirgin.

Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe a kauyen Asham da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna kuma jirgin ƙasa ta bar Abuja ne da misalin karfe 9:45.

Har yanzu ba a san abin da ya jawo saukar jirgin daga kan layin dogo ba, kuma babu tabbacin ko an samu waɗanda suka jikkata.

Hukumar Jiragin ƙasar Najeriya (NRC) bata yi tsokaci ba a kan lamarin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Masu yin aure da kananan shekaru ku daina, ku bari sai kun girma>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma Wakili

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *