Friday, December 26
Shadow

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna zai koma aiki nan da kwana 10 – Minista

Ministan sufurin Najeriya, Sa’idu Ahmed Alkali ya ce nan da kwana goma jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ya lalace zai koma aiki.

A makon jiya ne dai jirgin ƙasan ya kauce hanya, inda ya tunsture a kusa da tashar Asham bayan ya taso daga Abuja zai tafi Kaduna ɗauke da mutum 618, ciki har da har da fasinja 583 da ma’aikatan jirgin ƙasan guda 15 da ma’aikacin jinya 1 da masu goge-goge 11, sannan aƙalla fasinja bakwai ne suka ji rauni.

A wata ziyara da ministan sufurin ya kai wajen da jirgin ya kauce hanya a jiyar Litinin, ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da tsaron fasinjojin da sauran ma’aikatan jirgin har aka kwashe su.

Karanta Wannan  Wallahi mafi yawanci masoya Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) 'yan WiyWiy ne, saboda mune zaka gani gaba-gaba a wajan Maulidi, da Wazifa da salati>>Inji Wannan Dan Wiywiy din

“A lokacin da jirgin ya tuntsure, jirgin yana tafiya ne da tarago guda bakwai. Tuni mun kwashe guda huɗu, sannan muna ƙoƙarin kwashe sauran. Muna sa ran nan da kwana biyu za mu kwashe sauran taragon, sannan in sha Allah nan da kwana goma jirgin ƙasa zai koma aiki kamar yadda ya saba,” in ji ministan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *