
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyanawa shugaban kasar Israela, Benjamin Netanyahu cewa a bide iyakokin kasar Falasdinawa a kai musu agajin kayan abinci da sauran kayan Masarufi.
Ya bayyana hakanne a wata ganawa da suka yi ta wayar salula.
Trump yace Falasdinawa na cikin halin matsin rayuwa kuma ya kamata a kyautata musu.
Masu sharhi akan al’amuran yau da kullun sun bayyana cewa, wannan magana ba lallai tawa Benjamin Netanyahu dadi bane.
Hakanan a wani yanayi da ake kallon na mayar da Benjamin Netanyahu gefe, Trump yayi sulhu da mayakan kasar Yemen, sannan ya ci gaba da tattaunawa da kasar Iran kan makamashin kare danginta.
Hakanan Wani rahoto yace Trump ya nuna cewa baya bukatar Netanyahu wajan mu’amala da Gabas ta tsakiya.