Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, bai kamata mutane da suka kai shekaru 70 zuwa 80 ba su rika karya.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga maganar Atiku Abubakar ta cewa sun hada kai dan kwace mulki daga hannun APC a shekarar 2027.
Kwankwaso ya bayyana cewa wannan magana bai san da ita ba kuma jinta ya bata masa rai.
Yace wannan ne matsalar Najeriya.
ya kara da cewa, Jam’iyyar PDP ta mutu ne shiyasa take nema sai ta hada kai da wasu jam’iyyun kamin ta samu nasarar karbar Mulki.