
Cocin katolika reshen Birnin New York na kasar Amurka sun yi Allah wadai da shugaban kasar Amurka, Donald Trump saboda saka hotonsa sanye da kayan Fafaroma.
Donald Trump a safiyar jiyane ya dauki hankula bayan da aka ganshi sanye da kayan Fafaroma a wani hoto da fadar shugaban kasar ta White House ta wallafa a kafar X, hoton da aka yi amannar na AI ne.
A sanarwar cocin Katolika, tace bata dade da jimamin binne Fafaroma Francis ba kuma a yanzu ana kokarin zaben sabon Fafaroma dan haka Trump ya kiyayesu kada ya musu izgilanci.