Friday, December 5
Shadow

Ka shiga taitayinka, naga take-takenka baka a da’a>>Shugaba Tinubu ya gargadi Sanata Ali Ndume bayan da yace ‘yan Najeriya na cikin wahala

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Fadar shugaban kasar Najeriya ta gargadi Sanata Ali Ndume kan kalaman da yake yi wanda ta kira na rashin da’a ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Fadar shugaban kasar tace akwai rashin da’a a cikin kalaman na sanata Ali Ndume.

Sanarwar ta fito ne daga bakin me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga inda yace maganar da Sanata Ndume yayi cewa akwai masu satar kudin talakawa da wadanda basu cancanta ba a cikin gwamnatin Tinubu bai kawo wata hujja akan ta ba.

Yace Ndume na da ‘yancin fadar albarkacin bakinsa tunda yake shi dan adawane a cikin jam’iyyar APC, yace amma mafi yawanci Ndume na maganane akan abinda bashi da hujja akai.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda gaba dayan wani Qauye suka karbi Kalmar Shahada

Yace haka wajan bare-barensa yaje yace wai an kaiwa janar Tukur Yusuf Buratai hari.

Yace yawanci masu aiki da Tinubu kwararru ne wanda tun kamin a basu mukami a Gwamnatin an sansu a fannonin da suke aikinsu na kwarewa kuma suna taimakawa wajan ci gaban Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *