
Wata Kungiyar Yarbawa me suna Ìgbìnmó Májékóbájé Ilé-Yorùbá ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya wallafa sunayen mutanen da gwamnatinsa tace ta rika baiwa tallafin Naira dubu 25 duk wata.
Kungiyar ta bakin shugabanta, Olusola Badero tace wannan maganar duk farfaganda ce.
Tace ko da da gaske an bayar da wannan tallafin, idan aka duba, za’a ga cewa yawanci ‘yab jam’iyyar APC ne.
Tace dan haka a wallafa sunayen mutanen da aka baiwa tallafin da jihohin da suka fito.
Kungiyar tace ko da ma an bayar da tallafin da gaske, Naira 25,000 a wata ba zata iya ciyar da iyali ba, saboda buhun shinkafa ya haura Naira 70,000.
Kumgiyar tace tun da shugaba Tinubu ya hau mulki mutane a shiyyar Yarbawa suka fada yunwa da talauci inda da yawa sun koma roko kamin su samu abinci.