
Diyar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, Noor Buhari ta bayyana cewa, kabarin Babanta, yafi kujerar mulkin da ya bari haske.
Noor ta bayyana hakane a shafinta na Instagram inda tace tun rasuwar babanta zuciyarta ta yi nauyi kuma ga kadaici
Noor ta kuma wallafa Bidiyon ta tare da mahaifin nata inda tace tana rokon ‘yan Najeriya su saka mahaifinta a addu’a.