Thursday, January 9
Shadow

Kada ku yadda da sabuwar dokar haraji>>Sanata Ndume ya gayawa sarakuna

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yayi kira ga sarakunan dake karkashin mazabarsa da kada su yadda da sabuwar dokar haraji ta shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Ya bayyana hakane a yayin da ya kai ziyara Masarautar Askira, inda yace dalilinsa na kin amincewa da dokar harajin shine wahalar da mutane ke ciki, dan hakane yake kira da sarakunan da suma kada su amince da ita.

Yayi kira ga matasa da su tashi su rungumi harkar noma inda yace a daina dogaro da gwamnati da Albashi dan kuwa albashin Naira dubu 70 ba zai sayi buhun shinkafa ba dake Naira dubu 100 ko buhun wake dake Neman kaiwa Naira dubu dari 200.

Karanta Wannan  Yarinya ta yi Goshi: Yadda Ƴar Makaranta Da Aka Kòra Ta Shigo Gari. Ta Samu IPhone 16, Taje Umara, Yanzu Kuma Ga Sabuwar Mota GLK. Allah Ya Sanya Alkhairi

Ya jinjinawa mutanen garin Gwoza saboda jajircewar da suka nuna duk da matsalar tsaron da suke fama da ita inda yace babu yanda za’a yi a rika kawo musu hare-hare ba tare da masu bayar da bayanan sirri ba, yayi kira mutanen na Gwoza da su rika kamawa da lallasa masu baiwa ‘yan Bindigar bayanan sirri tare da mikasu hannun hukuma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *