
Kafar Axios ta kasar Amurka tace ta gano cewa shugaban kasat Amurka, Donald Trump karya yake da yace baya goyon bayan harin da aka kaiwa kasar Ìràn.
Kafar tace ta yi magana da wata majiya 2 daga Israyla wadda ta tabbatar mata da cewa sai da kasar Amurkar ta amince sannan suka kaiwa kasar Ìràn hari.
Kafar tace shugaban Amurka Donald Trump ya nuna cewa bai san da harin bane dan yaudarar wadanda suke son kashewa su tsaya kada su boye kamin a kashèsu.
Shugaba Trump dai yayi ikirarin cewa, ya gargadi kasar Israyla kada ta kaiwa kasar Iràn hari, amma idan wannan rahoton na kafar Axios ya tabbata, to lallai ya munafurci mutane.