
Wani magidanci ya bayyana cewa ya auro wata Bazawara me da daya.
Yace ya dauki nauyin karatin dan nata sannan ya mata albashi yana biyanta duk wata dalili kuwa shine tana aiki ya aureta amma yace ta daina aikin baya so zao rika bata Albashi.
Saidai yace basu dade da yin aure ba sai ya fara ganin Halayyarta ta fara chanjawa.
Yace sai ya ga tana waya amma bata son ya ji abinda take cewa.
Yace wata rana ya koma gida ba lokacin da ya saba komawa ba sai ya ga mota a kofar gidansa ta faka, koda ya duba sai bai ga matarsa ba, ashe itace a cikin motar.
Yace ya lakada mata dukan tsiya sosai.
Kalli Bidiyon inda malam Musa Asadussunnah ya bayar da labari.