Friday, December 26
Shadow

Kaine Zabin Kanawa a 2027, Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta baiwa shugaba Tinubu tabbaci

Jam’iyyar APC Reshen jihar Kano ta baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tabbacin goyon baya a zaben shekarar 2027 me zuwa.

Jam’iyyar ta kuma bayyana Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.

Sun bayyana hakane yayin wani zama da aka yi a gidan tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya bayyana cewa, an shirya taronne dan warware matsalolin cikin gida na jam’iyyar da kuma shiryawa babban zaben shekarar 2027 dake tafe.

Karanta Wannan  Bidiyo: Kaso 80 na matsalar Najeriya Gwamnoni ne saidai su yi ta rawar Omologo basa gayawa shugaba Tinubu gaskiya>>Inji Farfesa Usman Yusuf

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *