
Shahararren Mawakin Najeriya, Davido ya bayyana cewa duk kalar abincin daya ci, shine Direbansa da kowa da kowa yake ci a gidansa.
Ya bayyana cewa, matarsa na tabbatar da hakan inda yace irin tarbiyyar da aka masa a gidansu kenan.
Davido wanda mahaifinsa shahararren me kudine yace a baya babu wanda yasan mahaifinsa duk da yana da kudi amma da ya fara wakane ya rika fadin irin abinda mahaifinsa ya mallaka mutane suka fara sanin wanene mahaifinsa.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.