
Sheikh Adam Muhammad Albany Gombe ya yiwa shahararren dan soshiyal Midiya, Dan Bello Tonon Sililin da ya yi Alkawarin yi masa.
Hakan ya biyo bayan labarin da Dan Bello ya wallafa ne na zargin shugaban Izala, Sheikh Bala Lau da aikata ba daidai ba da dukiyar gina ajujuwan karatu.
A martanin Sheikh Adam yace Dan Bello bashi da alaka da wani babban malami ko makaranta dan haka bai ga dalilin da zai sa wanda bashi da ilimin addini mutane su rika daukar labari daga wajansa ba.
Malamai da yawa sun mayarwa da Dan Bello Martani masu zafi sosai.