Monday, June 2
Shadow

Kalli Bidiyo: An zargi Ana yiwa kananan yara maza fyade a gidan yarin Goron Dutse dake Kano

Wani faifan Bidiyo ya bayyana inda aka ji wani bawan Allah na ikirarin cewa ana yiwa yara maza fyade a gidan yarin Goron Dutse dake Kano.

Yace ana amfani da kananan shekaru da yaran ke da su da kuma bukata ta abinci da suke da ita ana lalata dasu.

Yace a wasu lokutan ma ana hada baki da wasu bata garin ma’aikatan gidan yarin ana basu kudi ana baiwa yaran a daukesu, yace a wasu lokutan kuma yawan kudin da za’a baiwa yaranne ke daukar hankalinsu su aikata wannan masha’a.

Yace yana kira ga hukumomi da su je su bincika abubuwan da ya fada inda yace akwai ma abubuwan da bai fada ba wanda ake yi a gidan yarin.

Karanta Wannan  Yan Nigeria kuji tsoron Allah ku daina Zargin Tinubu da cire Tallafin Man fetur, Saboda Bola Tinubu Ba shine ya cire Tallafin Man fetur Ba, Buharine>>inji Kawu Sumaila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *