
Babbar Jarumar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa’a ta karyata abokan sana’arta, Rukayya Dawayya da Saima Muhammad da suka fito suka nuna cewa, wai Rashin Biyayya ga iyaye ne ya jefa Ummi Nuhu halin data tsinci kanta a ciki.
Tace sun bata kunya, tace dukansu babu wanda bai yi tarayya da Ummi Nuhu ba a lokacin da take ganiyarta ta fi kowa rufin Asiri a masana’antar fina-finan Hausa.
Tace amma yau dan ta shiga wani hali shine suka gujeta, tace to ita ta san irin kyautatawar da Ummi Nuhu tawa mahaifiyarta, dan mahaifinsu bashi da rai.
Tace dinki bata san sau nawa Ummi Nuhu tana bata atamfa tana kaiwa a wa mahaifiyarta dinki ba.
Tace haka mahaifiyar Ummi Nuhu wai Lokacin zata ce tana son abu kasa kuma idan Ummi bata dashi, hankalinta zai tashi.
Tace daya daga cikin abinda ya lalata Ummi Shine kawaye.
Tace kuma karya suke suce ba da Ummi Nuhu suke ba maganganun da suka yi, tace a cikinsu babu wanda take jin tsoro.
Dukansu dai Rukayya Dawayya da Saima Muhammad basu kira sunan Ummi Nuhu ba a Bidiyonsu.