
Malamin Addinin Islama, Malam Lawal Triumph ya bayyana cewa, ‘yan jaridar da suka halarci wajan zaman majalisar shura sun bayyana cewa an aika su ne su cimma wata manufa.
Yace sun gaya masa cewa wallahi ko kusa basu yi tsammanin zai iya kare kansa kan kalaman da yayi ba.
Malam ya bayyana hakane a yayin da ya ci gaba da wa’azi bayan ya kare kansa a gaban majalisar Shura.