
Sanata Natasha Akpoti a hirar da aka yi da ita a kafar BBC ta bayyana cewa bata san me yasa wasu ‘yan Najeriya basa gane irin halin da take ciki ba.
Tace tana son ta samu guri ne da zata yi aiki ba tare da ana nemanta da lalata ba.
Tace Sanata Godswill Akpabio har ce mata ya taba yi mijinta na morewa dan da gani tana juya masa duwawunta da kyau.
Sanata Natasha Akpoti tace mata da yawa daga kasashen Africa daban-daban sun kirata inda suka rika gaya mata cewa suma suna fuskantar irin wannan cin zarafi a guraren aikinsu.
Tace maganar cewa bata bi dokar majalisa bane yasa aka dakatar da ita ba gaskiya bane.