Kungiyar ISWAP data balle daga jikin B0K0 Hàràm ta kaiwa sansanin sojojin Najariya hari a garin Damboa dake jihar Borno.
Maharan sun kona gidaje da motocin sojojin da kashe akalla sojoji 7.
Rahoton Sahara Reporters yace maharan sun shafe awanni 2 suna cin karensu ba babbaka a sansanin sojojin.
Rahoton yace harin ya farune ranar 4 ga watan Janairu, watau Asabar data gabata.
Wani soja yace zuwa yanzu sun gano gawarwakin Sojoji 7, kuma ya kara da cewa an kai musu harinne da misalin karfe 4 na safe.