Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo da Hotuna: Yanda ‘yan tà’adda suka kai hari sansanin sojoji a jihar Yobe, sun kàshè sojoji 4 da kona motocin yakin sojojin, daga farkon shekara zuwa Yanzu, Rahotanni sun bayyana cewa sun tashi sansanin sojoji sama da 8

Rahotanni sun bayyana a baya cewa, mayakan kungiyar Ìśìśì sun dauki alhakin kai harin da yayi sanadiyyar mutuwar sojojin Najeriya 4 da jikkata wasu a jihar Yobe.

Kungiyar ta kuma wallafa hotunan harin da ta yi ikirarin kaiwa.

An ga hotunan konannun motocin sojoji yayin da wasu kuma aka ga suna ci da wuta.

Kungiyar ta yi ikirarin kai hari da tarwatsa sansanin sojoji sama da 10.

Karanta Wannan  Hukumar Kula da jami'o'in Najeriya, NUC tace wadanda aka baiwa Digirin Girmamawa irin wadda aka baiwa Rarara su daina Amfani da sunan "Dr." A jikin sunansu

Saidai Maau shashi sun ce sansanin sojoji 8 ne suka tarwatsa daga farkon shekararnan zuwa yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *