
Tauraron fina-finan Hausa kuma MC Ibrahim Sharukhan Ya mayarwa da malamin Addinin Islama, Sheikh Lawal Triumph martani kan sukar ‘yan fim.
Da farko dai Tijjani Faraga ne ya bayyana cewa, Shi ba dan Iazala bane kuma duk wanda ya kara hadashi da Izala Allah ya isa.
Daga nan kuma sai Malam Lawal Triumph ya mayar masa da martanin cewa ai babu ‘yan fim da ‘yan Daudu, da Bokaye a Izala.
A martanin MC Ibrahim Sharukhan yace malam da yake zagin ‘yan Fim ya sani matarsa Allah ne kawai yayi ba zata yi fim ba amma tana da kawaye maza da mata ‘yan fim.
Lamarin dai ya dauki hankula.