
Babban Malamin Addinin Islama, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, da ya kammala aikin gwamnati a watan Mayu na shekarar 2023 ya tattara motocin gwamnati 6 da aka basu yana aiki dasu ya mayarwa da gwamnati kayanta.
Malam yace akwai wani abokinsa da ya gaya mai cewa ba’a mayarwa rikewa ake haka aka saba, saidai malam yace ya nuna masa inda yake rubuce a doka.
Yace indai ba doka bace ta zo dashi a rubuce dan haka shi yana ganin wannan motoci ba halas dinsa bane dan haka ya mayar dasu.
Malam ya bayyana hakane a yayin karatu da yake gabatarwa.