
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana irin muguntar da wani kamfani ya masa da ya bashi matsala sosai
Yace a lokacin suna gina matatar man sa, sun baiwa wani kamfanin da baiso ya ambaci sunansa kwangilar kawo musu kaya.
Yace kamfanin sai ya kawo kaya marasa kyau suka yi amfani dasu, yace kamin su gyara matsalar da abin ya basu sai da suka shekara 2.