
Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid wanda aka fi sani da Digital Imam ya bayyana cewa, ‘yan Darikar Sufaye su suka fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Malam yace abin ba zai yiwa wasu dadin ji ba amma dole a fadi gaskiya.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda yace asalin Sufaye sun samo asaline daga Zuhudu, watau Gudun Duniya.