
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu da labarin rayuwarta ya dauki hankula a kafafen sadarwa ta ja kunnen abokan sana’arta musamman masu tasowa.
Tace idan daukaka suke ji da ita ta samu amma yanzu babu komai.
Saidai ta nuna farin cikinta da irin soyayyar da aka nuna mata bayan hirar ta ta farko da Hadiza Gabon.
Ummi har kukan dadi ta yi.