
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, Tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na da yawan taimako amma matsalar da ake samu shine mafi yawan lokuta mutane na yaudararsa ne ko suna cin amanarsa.
Ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Yace Tunda yake da El-Rufai bai taba ganin yana kokarin siyasa kansa gida ba ko iyalansa, a ko da yaushe yana kokarin taimakon mutanene.
Yace dan haka suna tare dashi kuma zasu bashi kariya da goyon baya.
Da alama dai wannan tsohon Bidiyone dan kuwa tuni dangantaka ta yi tsami tsakanin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Gwamna Uba Sani inda El-Rufai ya fada a gidan talabijin na Arise TV cewa Uba Sani ba abokinsa bane, sun bata.