
Diyar tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari, watau Zahra Buhari ta bayyana cewa, mahaifinsu ya iya rikon gida.
Tace mutum ne wanda suke kallonshi a matsayin dama haka Namiji ya kamata ya kasance.
Tace yana musu sutura, abinci, kuma yana kula dasu yanda ya kamata.
Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita bayan rasuwar mahaifinta inda aka tambayeta ta fadi wasu abubuwa akan mahaifinta wanda ba kowane ya sani ba.
Ta kara da cewa mutum ne me Tauhidi.
A lokacin da ya rasu a Landan an ga yanda Zahra Buhari ta kwalla ihu akan titi.