
Babban Fasto, Fasto Adebayo yace yana baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar cewa ya je ya roki shugaban kasar Amurka, Donald Trump kada ya kawo harin da yakw shirin kawowa, ya bashi kwanaki 100.
Yace sai kuma Tinubu ya dawo Najeriya ya baiwa shuwagabannin sojoji umarnin su magance matsalar ko kuma a sauke su daga mukamansu.
Faston ya bayar da wannan shawara ne a yayin da yake wa’azi a cokinsa.