
Adam A. Zango ya yiwa abokan arziki godiyar ziyarar dubiya da aka rika je masa bayan hadarin da ya faru dashi, Adamu ya bayyana hakane a Bidiyon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Yace wasu sun je wasu kuma sun tayashi da addu’a saboda uzuri basu samu damar zuwa ba.
Yace bai ji wani rauni da zai zamar masa nakasa ba.