
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa daya daga cikin ayyukan da yakewa jihar Kano Shine baiwa matasa tallafin Naira dubu 50 a wata.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron siyasa.
Saidai matasan sun musanta wannan ikirari na gwamnan inda suka ce ba’a basu ko sisi.
Gwamnan dai yace zai yi bincike kan lamarin.