
Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Lawal Triumph ya bayyana cewa, irin murnar da ‘yan Shi’a ke yi da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari alamace ta cewa mutumin kirki ne.
Yace dan kuwa sun yiwa sahabbai irin zagezagen da sukewa Buharin.
Yace babu amfanin murnar mutuwa.
Yace kuma babu wanda zai mutu ba da hakkin wani ba ko zunubi.
Yace kuma Allah yace ku yafe dan shima ya yafe muku.
Yace kuma ko da kisan da akawa ‘yan Shi’a a Zaria yana kan daidai.