Sanata Uzor Kalu dake cikin majalisar dattawan Najeriya ya bayyana cewa Naira Miliyan 14 kacal ake biyansu a matsayin Albashi.
Ya bayyana hakane a wata gira da kafar Channels TV ta yi dashi inda yace kudin ma basa isarsu.
Yace a cikin wadannan kudadene suke biyan ma’aikatansu da shan mai da zuwa mazabunsu su yi aiki.
Da yake magana akan motoci masu tsada da aka ce an siya musu,yace ba gaskiya bane.
Yace motocin ba na hawansu bane,na aiki ne.