
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Lawal Triumph ya bayyana cewa, a wajan Hausawa ne Kwarkwata take zama alamar Talauci da Kazanta.
Yace amma a wajan Larabawa, Kwarkwata ba alamar Talauci da kazanta bace.
Yace me arziki ma sai a ganshi da Kwarkwata indai baya kula da kansa.
Malam ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu a kafafen sada zumuntan
Hakan na zuwane biyo bayan kaurewar mahawara bayan da malamin ya karanto Hadisin da yace an samu Kwarkwata akan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).